Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar a yammacin ranar jiya Alhamis ne ?an SHI’A mabiya Zakzaky suka fito kan titi domin kira ga gwamnati aka a sakar wa malaminsu fasfo ?insa na fita kasar waje domin neman magani.
?an shi’ar dai sun fito suna fa?in Free Zakzaky fasfo a daidai lokacin da tawagar Gwamnan jihar Nasiru El-Rufa’i ta zo wucewa ta wurin a yankin titin Byepass, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, lamarin da ya haifar da artabu tsakanin su da tawagar Gwamnan tsaro suka iso wajen su suna harba musu tiyagas ganin haka yasa mabiya shi’ar suka dinga fa?in Allahu Akbar daganan sai jami’an tsaron suka fara harbinsu da bindiga harsashi mai sai haka yai sanadiyar rasuwar mutane shida a cikin ?an shi’ar tare da raunata wasu da dama.
Ga sunayen wa?anda aka kashe a wajen.
(1) Aliyu Sulaiman
(2) Abubakar Nura(Abba)
(3) Ibrahim Abdullahi (Cash money)
(4) Yasir Isma’il Abduzzahara
(5) Abdulmalik Ibrahim (Yawale)
