Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulki ta sake tsunduma cikin ru?ani da rabuwar kawuna, inda shugabancin jam’iyyar ya bi sahun wasu gwamnonin ?asar da ke fito-na-fito da manufar daina kar?ar tsoffin ku?i ta Shugaba Muhammadu Buhari.
Bayan wani taro da Kwamitin Gudanarwar APC na kasa ya gudanar da yammacin jiya Lahadi, jam’iyyar mai mulki ta yi kira ga shugaban ?asar ya mutunta umarnin Kotun ?oli a kan wannan batu.
Taron wanda mahalartansa suka shafe kimanin tsawon sa’a biyar suna tattaunawa a hedikwatar APC ta ?asa, ya kammala ba tare da wani dogon bayani kan yadda al’amura suka kaya ba.
Sai dai fuskokin gwamnonin APC da suka halarci taron, babu annuri.
Haka zalika, sanarwar bayan taro da shugaban APC na ?asa ya karanta bayan fitowarsu, ta?aitacciya ce.
Wannan kuwa na zuwa ne adaidai lokacin da yake kwanaki kalilan a gudanar da babban za?e. Sannan al’umma na kokawa da yanayi matsin rayuwa da batun sauya kudi ya jefa su.
