Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar zabe ta INEC ta nesanta kanta da wata sanarwa da ke yawo mai cewa, za a daga zaben 2023 mai zuwa.
An yada wata jita-jita a ranar Litinin 13 Faburairu, 2023 cewa, hukumar zabe na duba yiwuwar dage zaben 2023 zuwa ranar 4 ga watan Maris na bana saboda karancin Naira da ake fuskanta.
Wani rahoton ya kuma ambato shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu na cewa, karancin kudin da ake fama dashi a kasar ya shafi hukumar kuma dage zaben ne mafi kyau ga ‘yan Najeriya.
“Ba gaskiya bane. INEC ba za ta yi ba, kuma ba ta tunanin dage babban zaben 2023. “Don kawar da shakku, za a yi zaben shugaban kasa/na ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 ga watan Faburairu, yayin da za a yi zaben gwamnoni/na ‘yan majalisun jihohi a ranar 11 ga watan Maris.”
