Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor ya yi i?irarcewa ba tun yau ba, an da?e ana yi wa sojoji da sauran jami’an tsaro romon kunne su ha?a baki a mur?e za?e.
Sai dai kuma Irabor ya ce sojoji tsaye su ke ?yam a wuri ?aya, a tsakiya, ba su goyon bayan kowace jam’îyya, kuma babu ruwan su da kowane ?an takara.
“Tabbas a kowane za?e tun bayan dawowar mulkin dimokra?iyya a 1999, sojoji na fama da matsin-lamba daga wasu ?atagari marasa kishi, su na so sojoji su ba su ?ofar yin magu?in za?e.
“Wa?annan marasa kishi ba wai a kan sojoji ka?ai su ka tsaya ba, har da sauran jami’an tsaro kamar su ‘yan sanda. To irin tsiyar su ke so a kowane za?e su ri?a tafkawa, mu kuma ba mu yarda da su.”
Irabor ya ce irin wannan matsin-lambar da sojoji ke sha ba za ta sare masu guiwa ba, sai ma ta ?ara masu kuzarin ?ara tashi tsaye wajen kare dimokra?iyya.
Ya yi wannan bayani a wurin taron Ganawar Ma’aikatu da Manema Labarai karo na 61 da ya gudana a Fadar Shugaban ?asa, wanda tawagar jami’an ya?a labaran Shugaban ?asa ke shiryawa.
Irabor ya yi wannan kalami ne lokacin da ya ke amsa wata tambaya daga manema labarai, inda ya ke tabbatar masu cewa sojoji ba za su ta?a goyon bayan wata jam’iyya ko wani ?an takara ba, kamar yadda su ke bisa wannan tsari tun daga dawowar mulkin siyasa a 1999.
“Na ji da?i da har ku ka ?ara jaddada wannan garga?in ?in daba kai borin masu neman sojoji su ba su ha?in ya hau, wanda Babban Kwamandan Askarawan Najeriya ya yi. Na ji da?in da ku ka ce ku na da damuwa. To amma mu dai tabbas duk inda gaskiya ta ke, to za a tsaya kan ta, kuma a fito da ita.
“Amma mu a ?angaren sojoji, ai ba da ka mu ke aiki ba. A bisa tsari, ?warewa da kuma bin doka mu ke aikin mu. Kuma a haka za mu ci gaba da kasancewa.