Kungiyar Likitoci Ta Yi Kiran Bincikar Kwakwalwar ‘Yan Takarar Shugabancin Kasa

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar likitoci ta ?asar ta yi kiran da a fara aiwatar da yin gwajin ?wa?walwa ga ‘yan takarar siyasa domin samar da shugabanni nagari.

Bayanin hakan na ?unshe ne a cikin wata takardar sanarwa da kungiyar ta fitar kuma aka rarraba ga manema labarai a Abuja.

Sanarwar ta bayyana cewar kiran ya zamo wajibi ta la’akari da irin fara sa?a da mugun zare da mafiyawancin ‘yan siyasa ke aikatawa.

“Tabbas matukar an ?auki wannan mataki za a yi nasara a kokarin da ake dashi na ganin an samu shugabannin da suka dace wa?anda za su yi kyakkyawar jagoranci domin kai ?asar gaba”.

Sai dai wannan mataki na kungiyar likitocin ya haifar da surutai a ?asar inda wasu ke ganin dacewar hakan yayin da wasu ke ganin akasi.

Related posts

Leave a Comment