Soke Takarar Aisha Binani: Ministar Mata Ta Nemi Daukin Buhari

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ministar al’amuran mata ta Najeriya Mrs Pauline Tallen, ta bu?aci shugaban ?asa Muhammadu Buhari da mai ?akinsa Aisha Buhari, da su sa baki a batun soke za?en fidda gwani na gwamna da jam’iyyar APC ta gudanar a jihar Adamawa.

Mrs Tallen ta yi kiran ne a lokacin wani taron ministoci da kamfanin dillancin labaran ?asar NAN ya shirya a Abuja babban birnin ?asar, ta kuma ce matakin soke za?en abu ne da ba za a lamunta ba.

Ta ?ara da cewa ”Soke za?en ‘yar takararmu ta gwamna mace ?aya tilo a Adamawa abu ne da ba za a amince da shi ba”.

Ta kuma yi kira ga ilahirin al’umma da su goyi bayan ‘yan takara mata a za?ukan 2023, domin samun ci gaban ?asa.

Related posts

Leave a Comment