An ?auki Alhakin Buhari Ba Shi Ya ?ara Farashin Mai Ba – Ministan Mai

?aramin ministan arzikin man fetur, Temipre Sylva, ya ce karin farashin man feturin da aka yi ba yin shugaba Buhari bane saboda dan tashi, ba za a taba kara farashin ba.

A ranar Laraba, kamfanin kasuwancin na PPMC ya sanar da tashin farashin mai zuwa N151.56. Bayan haka kuma, ‘yan kasuwan mai zasu kara nasu idan aka fara sayarwa N159 zuwa N162.

Yayin magana da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Temipre Sylva ya ce ba hakkin gwamnatin tarayya bane sanya farashin mai. Yace akwai takaici ‘yan Najeriya na daura laifin kan gwamnatin tarayya alhalin ita gwamnatin na kokarin kare mutuncinsu.

“Gwamnati ta cire hannunta cikin lamarin sanya farashin man fetur, mun janye,” NAN ta ruwaitoshi da cewa “Yanzu mun mayar da hankalinmu ne kan kare mutuncin ‘yan Najeriya wajen tabbatar da cewa ‘yan kasuwa basu samun riba fiye da yadda ya kamata.”

“Dukkanku kun san shugaba Muhammadu Buhari mutumin talakawa ne, musamman marasa galihu.” “Dan ta shi, ba zai taba bari a kara farashin man fetur ba, tun da kuka ga hakan ya faru, to abin ya fi karfinsa ne.

A bangare guda, Jam’iyyar APC ta daura laifin karin farashin man fetur kan jam’iyyar adawa ta PDP da gwamnatocinta na baya. Jam’iyyar mai ci ta yi raddi ne ga PDP yayindata ta soki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan kara farashin mai da na wutan lantarki lokacin da ‘yan Najeriya ke cikin halin talauci.

APC ta ce gwamnatocin PDP da suka shude ne suka sace arzikin kasar nan ta hanyar biyan tallafin mai, kuma hakan ke sabbaba matsalan da ake fuskanta yanzu.

Related posts

Leave a Comment