Matsalar Tsaro: Babban Lauya Ya Maka Buhari Da Majalisa Kotu

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar fitaccen Lauyan nan mai kare ha??in jama’a Femi Falana, ya maka Shugaba Muhammadu Buhari da Majalisar ?asa a Babbar Kotun Tarayya, inda ya nemi kotu ta tilasta masu gaggauta samar da na’urorin inganta tsaro a dukkan gidajen kurkukun Najeriya.

Ya maka su ?ara watanni biyu bayan ‘yan ta’addar ISWAP sun ragargaza kurkukun Kuje, inda su ka fitar da kwamandojin su 64, kuma wasu ?aurarru 800 su ka arce.

Falana ya ha?a har da Shugaban Gidajen Kurkukun Najeriya ya maka kotu, ya na so kotu ta jaddada masu cewa ha??in su ne su kare rayuka da lafiyar wa?anda ke tsare a gidajen kurkuku.

Ya nemi a samar da hasumiyar hangen mugaye daga nesa, doguwar katanga mai ?arfin Mahadi-ka-ture, kyamarar ?aukar hotunan bidiyon masu gilmawa a kusa da nesa, na’urar binciken jikin masu shiga da fita cikin kirkuku da sauran na’urorin gaggawa.

Falana ya buga misali da Sashe na 28 (1) na Dokar Gidajen Kurkuku ta ?asa, wadda ta nuna cewa gwamnati ce ke da ha??in kare su, ba wa?anda ke tsare ne ke da ha??in kare kan su ba.

Lauya Ayodele Aribisala na Ofishin Chambar Falana ne ya shigar da ?arar a madadin mai ?arar.

An shigar da ?arar a ranar 23 Ga Agusta, inda ya ro?i kotu ta tilasta wa wa?anda ya ke ?ara su bi abin da doka ta tanadar wajen kare rayuka da lafiyar wa?anda ke tsare a kurkuku.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Minista Rauf Aregbesola ya ce akwai jami’an tsaro 65 lokacin da ‘yan ta’adda su ka mamaye wurin.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya ce akwai jami’an tsaro 65 masu ?auke da makamai, a lokacin da ‘yan ta’adda su ka kai wa Kurkukun Abuja da ke Kuje hari watannin baya.

Aregbesola ya yi wannan bayani ranar Litinin a gaban Kwamitin Ha?in-guiwar Majalisar Tarayya.

Ya ce jami’an da ke wurin su 65 sun ?unshi sojoji, NSCDC, na Hukumar Cikin Gida da sauran jami’an wasu ?angarorin tsaro.

An dai kai harin a ranar 5 Ga Yuli, inda sama da ?aurarru 800 su ka tsere, cikin su kuwa har da ‘yan Boko Haram wajen 64.

ISWAP, ?angaren Boko Haram da su ka ?alle daga ?angaren Shekau sun ce su ne su ka ?auki nauyin kai harin, wanda washegari har bidiyon yadda fasa bango da ?ofar gidan kurkukun sai da su ka watsa.

An ri?a mamakin yadda su kayi nasarar kai harin duk kuwa da cewa akwai dandazon sojoji a yankin Gundumar FCT.

Related posts

Leave a Comment