Rahotannin dake shigo mana daga Ikko babban birnin Jihar Legas na bayyana cewar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Laraba ya bu?aci ?an Najeriya da su tabbatar sun za?i shugabanni na gari a za?ukan 2023.
Ya yi garga?in cewa idan har aka yi za?en tumun dare to ?asar na iya rushewa.
Obasanjo ya yi wannan magana ne a matsayinsa na babban ba?o a wajen wani taro da aka yi a Lagos.
Tsohon shugaban ?asar ya bayyana cewa yana fatan idan har aka za?i shugabannin da suka dace a 2023, to ?asar za ta ga ci gaba mai yawa.
“Idan har muka za?i shugabanni na gari a 2023 to tabbas za mu kai ga ci.”
“Amma idan muka yi za?en tumun dare to lallai za mu dilmiye,” a cewar Obasanjo.
Tun da fari sai da Obasanjo ya yi bayanin cewa ?asar ba ta ?aukar matakan da suka kamata wajen ya?i da talauci da rashin tsaro.
