Babban Bankin Duniya World Bank, a ranar Laraba ya yi gargadin cewa Najeriya na fuskantar barazanar da za ta iya rusa ta.
Bankin ya yi gargadin cewa idan Najeriya ta gagara gyara tsarin tara harajinta da kuma mayar da hankali akan wasu bangarorin domin bun?asa ku?a?en shigarta, to ?u?a?en shigarta za su ci gaba da raguwa.
An ruwaito wani babban jami’i a Babban Bankin Duniyar, Mr Rajul Awasthi ne ya bayyana haka a wani taro akan muhimmanci yi wa tsarin haraji kwaskwarima domin cigaban kasa, wacce wata kungiyar sa ido kan tattalin arzikin Najeriya ta shirya.
Sannan jami’in ya ha?i?ance cewa dole Najeriya ta cire tallafin man fetur baki daya nan gaba.
Bankin ya bayyana cewa duk da cewa farashin man fetur na ?aruwa a kasuwannin duniya, Najeriya ba ta samu cin gajiyar wannan dama ba saboda ma?udan kudaden da take kashewa akan rarar man fetur.
