Labarin dake shigo mana daga Lafiya babban birnin Jihar Nasarawa na bayyana cewa gwamnan Jihar Abdullahi Sule ya bayyana damuwa game da yadda gungun ‘yan fashin daji ke tururuwa zuwa jiharsa bayan koro su daga ma?wabtan jihohi.
Gwamna Abdullahi Sule ya ce jami’an tsaro sun lura da ?aruwar ‘yan bindiga a ?aramar hukumar Karu, wadda ke da nisan ?asa da kilomita 30 daga Abuja babban birnin ?asar.
“Mun lura da tarin ‘yan fashin nan da aka koro daga jihohin Kaduna da Katsina da Neja da Kebbi musamman a yankunan Rugan Juli da Rugan Madaki da ke ?aramar Hukumar Karu,” a cewar gwamnan yayin taron manema labarai ranar Asabar.
“Kazalika, mun ga wasu daga cikinsu a ?ananan hukumomin Wamba da Toto.”
Haka nan gwamnan ya ce sun yi nasarar kama wasu daga cikin fursunonin da suka tsere daga Gidan Yari na Kuje a Abuja bayan maya?an Boko Haram sun fasa shi a watan Yuni.
