Babban bankin kasa wato CBN, da hadin gwiwa Kamfanin Bizi Mobile cashless consultant limited, karkashin jagorancin shugaban kamfanin, Dr Aminu Bizi, sun shirya taron kaddamar da shirin e-Naira na farko a Jihar kano. Taron wanda akayi ma lakabi da ‘kano e-Naira week. Ya gudana ne a karkashin jagorancin shugaban bankin kasa wato CBN, Mr Emefele, wanda ya sami wakilci Mr Bosha Ernest daga hedikwata Abuja
A yayin da yake jawabi, shugaban kamfanin Bizi Mobile, Dr Aminu Bizi ya bayyana cewa, shiri ne da gwamnati tarayya ta kaddamar domin saukake ma Al’umma yawan rike kudade a hannu su, saboda irin hatsarin da tattare da hakan. Ya kara da cewa, alal misali, Babban bankin kasa wato CBN na kashe naira dubu biyu akan buga ko wane naira dari biyu, sannna ko wane kudi ana sa ran zai yi tsawon shekara biyu, amma kasancewar yadda ake tozarta kudin, bai wuce shakara daya ya lallace, dole a mayar da shi banki domin a kona.
Dr Aminu Bizi, ya ci gaba da bayyana cewa, ga yawan kashe kudin da Babban bankin kasa ke yi wajen dagon kudin, daga Abuja zuwa sassan jihohin kasar nan.
Ya kara da bayyana cewa, ana sa ran wannan shiri zai samarwa da dumban matasa ayyukan yi, wanda zasu dogara da shi, fiye da jiran aikin yi daga gwamnati.
Shima a nasa jawabin, Babban bako a wajen taron kaddamar da shirin na e-Naira, Kontrola mai kula da ofishin fasfo na kasa dake Kano, CIS Liman Sani Kila, ya jinjina kamfanin Bizi Mobile karkashin jagorancin Babban bankin kasa wato CBN, a bisa namijin kokarin da sukayi wajen shirya wannan taron.
CIS Liman Sani Kila, ya kuma kaddamar da gidauniyar marayu da marasa galihu wanda kamfanin Bizi Mobile ya horar da su akan harkokin hada hadar kudi irin na zamani wanda a turance ake kira da financial inclusion.
A yayin da yake nasa jawabin, shugaban Babban bankin kasa wato CBN Mr Emefele wanda ya sami wakilci Mr Bosha Ernest, ya bayyana makasudin kirkiro da shirin e-Naira, domin tafiya dai dai da zamani.
Mr Emefele, ya kuma kara da bayyana cewa, yana kira ga Al’ummar kasar nan da su rungumi wannan shiri domin zai kawo masu sauki cikin lamuran hada hadar kudi da suke gudanarwa. Sannan an tsaurara matakai ta yadda babu wanda zai iya yin kutse a asusun ajiyar kudin kowa.
Daga karshe, shugaban bankin kasa Mr Emefele, ya yaba ma kamfanin Bizi Mobile a bisa yadda suke wayarwa Al’umma kai akan abin da ya shafi sabbin tsare tsare domin ci gaban Yan kasa baki daya.
A yayin gudanar da taron kaddamar da shirin na e-Naira, an karrama wasu daga cikin shahararrun Mutane da suka sadaukar da rayuwar su wajen bautama kasa da Al’ummar su.
Wandanda aka karrama sun hada da;
CIS Liman Sani Kila, wanda aka karrama shi da Babban lambar yabo akan yadda ya sadaukar da rayuwar sa wajen taimakon kasa da kuma Al’ummar sa baki daya.
An kuma zabi wasu daga cikin jaruman masana’anatar shirya fina finai ta Arewa, a matsayin wanda zasu kasance jakadun e-Naira ta kasa.
Jaruman sun hada da; Lawal Ahmed, Alhaji Mustafa Naburaska, Daddy Hikima (Abale) Shuaibu Idris Lilisco, Ahmed Isa Ko-ko, Ado Gwanja da dai sauran su.
