Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar reshen ?alibai na Gamayyar ?ungiyoyin Farar hula na Arewa, CNG-SW sun yi barazanar rufe filayen jirgin sama da tashoshin jirgin ?asa da manyan titunan Arewa in har gwamnatin tarayya da ASUU ba su sansata an janye yakin aikin da suke yi ba.
?aliban sun kuma yi barazanar rufe ofisoshin jam’iyyun siyasa a jihohi 19 na yankin Arewacin Nijeriya.
?ungiyar ta yi wannan barazana ne a wata takardar bayanin bayan taro, wanda Kodinetocin kungiyar na jihohi 19 su ka gudanar ranar Juma’a a Kano.
Da ya ke karanta takardar ga manema labarai, Kodinetan kungiyar na ?asa, Jamilu Charanchi ya ce ?ungiyar ta cika da damuwa bisa yadda yajin aikin ASUU da na kwalejojin ilimi ya ci tura.
A cewar ?ungiyar yajin aikin ya jefa ?a?an talakawa cikin wata irin mawuyaciyar rayuwa.
Kungiyar ta ?ara da cewa tuni ta ?auki gabaran rubuta ?orafi ga Sarakunan gargajiya, malaman addini, jami’an gwamnati da jami’an tsaro a kan su saka baki a kawo karshen yakin aikin.
“Idan haka ba ta samu ba, to za mu rufe filayen jirgin sama da tashoshin jirgin ?asa da manyan titunan Arewacin Nijeriya.
“Za kuma mu rufe ofisoshin jam’iyyun siyasa a jihohi 19 na yankin Arewa,” in ji su.
