Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya ce kararrrakin da ‘yan adawa suka kai shi kotu lokacin da ya lashe zaben gwamna a karon farko su ne suka hana shi aiki sosai a jihar.
Ya bayyana haka ne a cikin shirin A Fada A Cika, na gidan Rediyon BBC Hausa.
Gwamna Yahaya Bello ya ?ara da cewar “Nasarar da muka samu a karo na biyu ta fi ta shekara hudu da muka yi a baya… mun yi aiki sosai amma saboda an kai mu kotu, an raba mana hankali.
“Shari’u ashirin da daya muka yi bayan zabe har zuwa Kotun Koli.”
Sai dai gwamnan ya ce a wa’adinsa na biyu ya fi gudanar da ayyukan inganta rayuwar jama’a saboda bai fuskanci kalubalen shari’a ba.
