2023: Adalci Shi Ne A Ba Mace Mataimakiyar Shugaban Kasa – A’isha Buhari

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Uwargidan Shugaban ?asa, A’isha Buhari ta yi kira ga dukkan jam’iyyun da zasu kafsa a za?en shugaban ?asa na 2023, su tsayar da mace a matsayin ‘ysr takarar mu?amin Mataimakiyar Shugaban ?asa.

A’isha ta yi wannan kalami ne a lokacin da ta ke jawabi wurin taron bu?e-baki da ta gayyaci ‘yan takara daga jam’iyyu daban-daban.

An yi taron a ranar Asabar da dare, a Fadar Shugaban ?asa, a Abuja.

Taron dai an shirya shi domin neman lada alfarmar watan Ramadan, inda ‘yan takara daban-daban za su gana da juna, su ?ara dan?on zumunci da ?aunar juna, a ?o?arin ?ara gina ?asa.

A’isha ta ce adalcin da ya kamata a yi wa mata a yanzu, shi ne a ?ara masu damar shiga cikin gwamnati da shugabancin manyan mu?amai.

“Lokaci ya yi da za a fara bai wa mata mu?amai, ana ba su guraben mataimakin shugaban ?asa, mataimakin gwamna, majalisa har ma da ?ananan hukumomi.

“Yayin da mu ke ta tseren kaiwa ga za?en 2023, ina da ya?inin cewa Najeriya za ta ci gaba da bun?asa sannu a hankali a bisa turbar dimokura?iyya.” Inji A’isha.

Daga nan sai ta yi kira ga duk ‘yan takarar shugaban ?asa su maida hankali wajen ?arfafa ha?in kan Najeriya, ?arfafa zumunci da kusantowar juna.

Ta tunatar da su cewa za?en 2015 wani al’amari ne muhimmi a tarihin Najeriya.

“Saboda shi za?en 2015 ba a tsaya ja-in-ja har aka je kotu ba. Haka ra’ayoyin jama’a ma duk a ?angare ?aya suka karkata, babu wata tankiya.

“Saboda haka babbar kyautar da ‘yan Najeriya za su yi wa iyalan Shugaban ?asa shi ne a gudanar da za?e sahihi, kuma kar?a??e a cikin Najeriya da duniya baki ?aya, a 2023.”

Daga nan kuma ta yi kira a guji tashe-tashen hankula musamman lokutan ya?e-ya?en neman za?e.

Related posts

Leave a Comment