Buhari Zai Sake Ciyo Bashi Domin Cike Gibin Kasafin 2022

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Buhari ya rubuta wasika ga Majalisar Tarayya yana neman a bashi damar sake ranto kudi daga waje don cike gibin da ke kasafin kudin 2022.

Buhari ya bayyana hakan ne cikin wasikar da kakakin majalisar dokokin tarayya Femi Gbajabiamila ya karanto yayin zaman majalisar a ranar Alhamis.

“Kamar yadda ka sani Kakakin Majalisa, sabbin sauye-sauyen da aka samu da tattalin arzikin duniya da na gida Najeriya ya tilasta dole a yi garambawul ga tsarin samar da kudi da kasafin kudin 2022 ya dogara a kai.

“Ana kyautata zaton gibin da za a samu a kasafin kudi ya karu daga Naira Biliyan 965.42 zuwa Naira Tiriliyan 7.35 wanda hakan shine kashi 3.99 cikin 100 na GDP a kasar.

“Za a cike gibin da aka samu a kasafin kudin ta hanyar ciyo sabbin bashi daga kasuwanni na gida. “Duba da bukatar da ke akwai na yin garambawul ga kasafin kudi na 2022.

Related posts

Leave a Comment