‘Yan Jarida Ne Sirrin Nasarar Ma’aikatar Jin ?ai – Sadiya

Ministar ma’aikatar Agaji Da Jin?ai, Hajiya Sadiya Umar Faroukh, ta yaba da ?o?arin kafafen ya?a labarai, ma’aikatan agaji da hukumomin ha?in gwiwa a daidai lokacin da ma’aikatar ta ta cika shekara ?aya da kafawa.

Ita dai wannan ma’aikata, Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ne ya ?ir?ire ta a ranar 21 ga Agusta, 2019 domin aiwatar da manufofi da ayyukan agaji, da rigakafin aukuwar bala’o’i tare da kai agajin gaggawa, sa’annan da gudanar da aikace-aikacen taimaka wa jama’a mabu?ata.

A cikin wata takardar sanarwa da mai agaza mata a harkar aikin ya?a labarai Halima Oyelade ta raba, ministar ta yi la’akari da cewa “wannan shekara ce da aka yi abubuwa da dama, mai cike da ?alubale da abubuwan sha’awa wadda a cikin ta mu ka koyi hanyoyin kai agaji ga jama’a da kula da bala’o’i, amma a duk cikin ayyukan mun maida hankalin mu wajen cika aikin da aka ba mu wanda ya ?unshi kai wa jama’a ?auki, hana aukuwar bala’i tare da agaza wa wa?anda bala’i ya auka mawa, da kuma fito da hanyoyin rage ra?a?in bala’i idan ya faru, wanda hakan ya taimaka mana wajen inganta aikin mu saboda nan gaba.”

A lokacin da ta ke yaba wa Shugaban ?asa a kan hangen nesa da ya yi na ?ir?iro ma’aikatar wadda ta kasance kan gaba wajen ya?i da annobar korona, Hajiya Sadiya Umar Farouq ta gode masa saboda ?ora ta a kujerar direbar ma’aikatar da ya yi.

Haka kuma ta yi la’akari da cewa a cikin wannan shekara ?ayan, ta koyi muhimman darussa tare da samun sabuwar fahimta game da hanyoyi masu ?ullewa da marasa ?ullewa a wannan aiki.

Yayin da ta ke yaba wa kafofin ya?a labarai, ministar ta ce wa?annan kafofi abokan tafiya ne wa?anda tilas ne a ha?a ?arfi da su don samun nasara.

Ta ce, “Ina so in bayyana maku a yau cewa aikin da ku ke yi ya dace.”

Ta ce da yake ba hurumin ta ne ta bai wa kan ta maki kan nasarorin da ta samu ba, amma a shirye ta ke ita da abokan aikin ta za su ci gaba da aikin su a cikin sadaukarwa da jajircewa don cika al?awurran aikin su, wanda ya yi daidai da jigon cikar su shekara ?aya – wato Service2Humanity.”
Ministar ta yi jinjina na musamman ga “ma’aikatan agaji da kuma abokan ha?in gwiwar mu a wannan sashe daga hukumomin Majalisar ?inkin Duniya irin su OCHA, IOM, UNHCR da Hukumar Abinci ta Duniya, Bankin Duniya, USAID da Tarayyar Turai (EU), da kuma sauran hukumomin ha?in gwiwa wa?anda su ka ci gaba da bada agaji duk da halin rashin tsaro da ake ciki da kuma wahalhalun da su ke fuskanta.

Ta kuma yi jaje kan wa?anda su ka rasu a wuraren da ake da rashin tsaro a cikin wannan shekara ?ayar da ta gabata.

Ministar ta yi bayanin cewa cika shekara ?aya da ?ir?iro ma’aikatar ya sa tilas su dage sosai.

Ta ce, “A yayin da mu ke murnar cika shekara ?aya, ina so in ce lokaci ya yi da ya dace mu sake zage dantse wajen aiwatar da aikin mu. Dole ne mu nemo hanyoyin da za mu fa?a?a aikin kula da bala’o’i, samar da agaji da kuma fito da hanyoyin tallafin jama’a wanda hakan zai taimaka mana wajen inganta aikin mu a nan gaba.”

Related posts

Leave a Comment