Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sanata Sa’idu Muhammad Dansadau shugaban kwamitin Masallacin Rukunin Gidajen Yan Majalisu na Apo, ya ce sun kori Sheikh Nuru Khalid daga limancin masallacin gaba ?aya.
Sanata Dansadau ya shaida wa BBC Hausa cewa sabon matakin ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa Sheikh Khalid din ne a ranar Asabar 2 ga watan Afrilun nan.
A wata wasi?a da kwamitin masallacin ya fitar a ranar Litinin mai ?auke da sa hannun Sanata Dansadau da aka aike wa Digital Imam, ya ce an ?auki matakin korarsa ne gaba ?aya saboda ?in yin nadamar da Sheikh Nuru ya nuna bayan dakatar da shi ?in.
Wasi?ar ta ce: “Akaramakallah ka fi ni sanin koyarwar Musulunci, manufar ladabtarwa ita ce don a gyara ?abi’ar mutum.
“Abin takaici, martanin da ka mayar kan dakatarwarka ta nuna cewa, balle ma har ka nuna nadama kan abubuwan da ka fa?a.
“Shugabanci na bu?atar sauke ha??i ka’in da na’in. Idan kalamanmu sun ?ata wa ?an ?asa rai fiye da faranta musu, to akwai hakki a kanmu na ?aukar matakin da ya dace saboda al’umma.
“Ga dukkan alamu kuma kamar ba ka da niyyar gyara hu?ubarka ta ranar Juma’a ta yadda za ta yi daidai da halin rashin tsaro da ake ciki a Najeriya,” in ji sanarwar.
A hirarsa da BBC Sanata Dansadau ya ce “malamin ya nuna cewa ko da kwarar zarra bai yi nadama ba ga abubuwan da ya yi, don haka bisa haka ba mu iya zama da shi.
“Ibada ce ba ma iya bin shi Sallah, kuma nafsi ya yarda idan ba ka iya bin mutum Sallah kana da damar ka sake Masallaci,” in ji shi.
Sanatan ya ?ara da cewa “Masallaci wurin ibada ne, ba wurin sukar gwamnati ba ne.”
