2023: Ku Guji Mayaudaran ‘Yan Siyasa – Obasanjo

Tsohon Shugaban ?asa Obasanjo ya bayyana hakan ne a jihar Legas yayin taron murnar cikar Fasto Itua Ighodalo, shekaru 61 da Haihuwa.

A cewarsa, matsalar Najeriya daya ce, kuma itace shugabanci. Yace: “Yau, suna biyan Naira Miliyan 40 sayen fom na takara Wasu na cewa wasu matasa ne suka saya musu.

Kai, duk wanda ya muku wannan karyan kada ku zabeshi wadanne matasa suka tara Naira Miliyan 40? Idan kana son siya, ka siya. Babu bukatar yi mana karya.”

“Idan ka tambayeni menene matsalar Najeriya, amsar ita ce shugabanci, Idan ka tambayeni menene mafita, shugabanci ne.” A cewarsa, ko Najeriya ta tattara dukkan kundin tsarin mulki mafi kyau a duniya, idan ba’a samu mutanen kirkin da zasu aiwatar da su ba, babu wata cigabar da za’a samu.

Related posts

Leave a Comment