Shugabancin Abdullahi Adamu Haramtacce Ne – PDP

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi wa APC gori tare da gwasale shugaban jam’iyyar da aka na?a a wurin Gangamin Taron ranar 26 Ga Maris, a Abuja.

Gangamin dai bai tafi daidai yadda aka tsara shi ba, domin da dama sun nuna ?acin rai dangane ya yadda ta kaya har aka fitar da shugabannin ba tare da an yi abin da su ke ganin cewa hakan ya fi dacewa ba.

Da yawa sun ri?a kukan cewa an cuce su, an na?a masu ba abin da su ka so ba.

A nata raddin, PDP ta yi wa APC gwalo da shagu?e cewa shugabancin sabon shugaban, Abdullahi Adamu haramtacce ne, kuma an dam?a jam’iyyar a hannun mai guntun kashin cin hanci, rashawa da wawurar ku?a?e a cikin wandon sa.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Ya?a Labaran PDP, Debo Ologunagbe ya yi kaca-kaca da APC da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, wadda ya ce ta ?aure gindin dam?a shugabancin APC ga kurar da bai kamata a ba ta ajiyar nama ba,

PDP ta ce ya kamata Abdullahi Adamu ya fito ya yi wa duniya bayanin inda Naira biliyan 15, wadda aka nema a hannun sa, shi da wasu jami’an gwamnatin Nasarawa su 19 da EFCC ta caje su da hutuma 149.

“Murnar da APC ke yi wai ta na?a shugaba ko shugabanni, ba murna ba ce, shewar-dila ce. Su na murna ne a kan yadda cin hanci da rashawa su ka yi galaba a kan batun ci gaban ?asa.

“Wannan taro ya nuna yadda gwamnatin Buhari ta ?aure wa cin hanci da rashawa gindi ta hanyar yaudara aka na?a shugabanni haramtattu a bisa jagorancin haramtacce, Abdullahi Adamu.

“Hakan da gwamnatin APC ta yi, ya nuna cewa ‘yan Najeriya za su ci gaba da rayuwar matsin tattalin arziki da ?unci har tsawon shekara ?aya kafin mulkin APC ya ?are.”

Idan ba a manta ba dai PDP ta maka APC kotu a ranar jajibirin Gangamin Taron APC a Abuja.

Related posts

Leave a Comment