Zamfara: ‘Yan Majalisa Sun Amince Da Tsige Mataimakin Gwamna

Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar na bayyana cewa Majalisar Dokokin Jihar ta jefa ?uria’r amincewa da tsige Mataimakin Gwamnan Mahdi Aliyu Gusau daga kan mu?aminsa da gagarumin rinjaye.

Yayin wani zama a jiya Alhamis, ‘yan majalisa 18 cikin 22 ne suka amince da ?aukar matakin yayin da ?aya tak ya ki amincewa.

Haka nan, ‘yan majalisar sun nemi Al?alin Al?alai na Zamfara Mai Shari’a Kulu Aliyu ya kafa Kwamitin da zai binciki Mahdi bisa zargin sa?a sashe na 190 da 193 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Dangantaka tsakanin mataimakin gwamnan da uban gidansa Gwamna Bello Muhammad Matawalle ta yi tsami tun lokacin da gwamnan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a bara amma Mahdi ya ci gaba da zama a PDP.

Related posts

Leave a Comment