Adamawa: An Bukaci Gwamnatoci Da Tallafawa Kamfanoni Masu Zaman Kansu

An kirayi gwamnatin tarayya dana jihohi da su maida hankali wajen tallafawa kanyfanoni masu zaman kansu domin ganin an samu cigaban harkokin kasuwanci yadda ya kamata, a fadin Najeriya baki daya.

Shugaban Kungiyar ‘yan kasuwa na arewacin Najeriya Alhaji Muhammed Ibrahim 86 ne yayi wannan kira a zantawarsa da muryar ‘yanci a Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa.

Alhaji Ibrahim 86 yace tallafawa kamfanoni masu zaman kansu zai taimaka matuka musammanma rage rashin aikin yi a tsakanin matasa, bunkasa tattalin arziki harma da wanzar da zaman lafiya mai dorewa.

Ibrahim 86 yace infa har gwamnatoci zasu taimaka wa kamfanoni masu zaman kansu to ba shakka za a samu saukin rayuwa dama saukin tsadar kayayyaki da yanzu ya zamewa al’umma matsala.

Ya kuma shawarci masu kamfanonin dake da zaman kansu da su kasance masu hada kansu a koda yaushe domin samun cigaban da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa baki daya.

Harwa yau ya kirayi matasa dake fadin Najeriya da su kasance masu bada tasu muhimmiyar gudunmawa domin samun hadin kan kasa dama cigaban kasan baki daya.

Ya kuma kirayi ‘yan Najeriya da su cigaba da yin addu’o’i a koda yaushe domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin matsalar tsaro a fadin Najeriya.

Related posts

Leave a Comment