Layukan Waya Miliyan 70 Basu Da Rajistar Ajiyar Banki A Najeriya

Rahotanni dake shigo mana daga Ikko Babban Birnin Jihar Legas na bayyana cewar an nuna damuwar cewa a?alla layukan waya miliyan 70 ne ba a ha?a su da lambar ajiyar banki ba, wato BVN.

Shugaban Kamfanin Hada-hadar Zamani na eTranzact, Niyi Toluwalope ne ya bayyana haka a Lagos.

Toluwalope ya yi wannan i?irarin a lokacin da ya ke jawabi a Taron Shekara-shekara na ?ungiyar ‘Yan Jarida Masu Aika Rahotannin Hada-hadar Kasuwanci ta Najeriya (CAMCAN), taro na 24 da aka shirya a Legas.

Ya ce mutum miliyan 150 a cikin mutum miliyan 200 duk su na da waya a Najeriya.

“Wa?annan mutane miliyan 150 su na da layuka miliyan 110. Amma daga cikin su, layuka miliyan 40 ne ka?ai aka ha?a da rajistar lambar ajiyar banki ta BNV.”

Toluwalope ya ?ara da cewa layuka miliyan 70 duk haka nan su ke zi?au, ba a ha?a su da kowace lambar BVN ba.

A kan haka ne ya ce akwai matu?ar bu?atar janyo miliyoyin mutane masu ?ananan harkoki su rungumi tsarin ajiya a banki, su bu?e asusu tare da lambobin wayoyin su.

Ya ce yin hakan zai taimaka wajen bun?asa ?ananan kasuwanci da ma manyan harkokin baki ?aya.

Ya ce kamata ya yi a tashi tsaye a zaburar da masu ?ananan kasuwanci ko sana’o’i alfanun tsarin hada-hadar zamani wajen bun?asa tattalin arziki, ta hanyar amfani da bankuna a sau?a?e.

Har yanzu dai ?ofa a bu?e ta ke wajen yi wa layukan wayoyin rajista, tare da ha?a su da lambar BVN ta banki.

Ita lambar BVN, sai idan ka bu?e asusun ajiya a banki za ka iya mallakar ta.

Related posts

Leave a Comment