Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya na?a Alaramma Ahmed Sulaiman kwamishina na biyu a hukumar kula da makarantun firamare ta jihar Kano.
Alaramma Ahmad Sulaiman ne ya tabbatar da ba shi wannan mu?amin a sa?on da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya yi godiya ga gwamnan.
Ya wallafa hotunansa tare da gwamnan, a gefe akwai Sheikh Abdullahi Balalau wanda shi ne shugaban ?ungiyar Izala, da kuma sakataren ?ungiyar na ?asa Sheikh Kabir Gombe.
Malam Ahmad Sulaiman ya ro?i Allah ya sa albarka a kujerar da ya samu da kuma ro?on addu’ar jama’a kan taya sa ri?o.
