Sakin Nnamdi Kanu Na Bukatar Dogon Nazari – Shugaban Kasa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai yi nazarin bu?atar da ya kira “mai girman gaske” ta neman ya saki Nnamdi Kanu wadda ?ungiyar dattawan al’ummar Ibo suka gabatar masa.

Kanu wanda ake zargi da aikata ta’addanci a gaban kotu, na hannun ‘yan sandan farin kaya na DSS sakamakon gwagwarmayar da yake yi ta neman kafa ?asar Biafra a kudancin Najeriya ?ar?ashin ?ungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da aka haramta.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake kar?ar ba?uncin dattawan a fadarsa da ke Abuja ranar Juma’a ?ar?ashin jagorancin tsohon Ministan Sufurin Jirgin Sama Mbazulike Amaechi.

“Kun nemi abu mai matu?ar girma a wajena a matsayina na shugaban wannan ?asa. Tasirin bu?atar taku na da girma sosai,” a cewar Buhari cikin wata sanarwa da Femi Adesina ya fitar.

Ya ?ara da cewa bu?atar da dattijan suka nema “ta sa?a wa tanadin tsarin mulki da ya fayyace tsarin shugabanci tsakanin gwamnati da ?angaren shari’a”.

“Sai dai bu?atar da kuka gabatar mai girma ce sosai amma zan yi nazari a kanta,” in ji shi.

Related posts

Leave a Comment