Mai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Mera a ranar Lahadi ya na?a Ministan Ya?a labaru da Al’adu na ?asa Lai Mohammed a matsayin Kakakin Kabi, ma’ana wakilin al’adar Kabi.
Kamfanin Dillancin Labaru na ?asa ya bada rahoton cewa na?a sarautar wadda ta faru a a fadar mai martaba sarkin Argungu dake Argungu a jahar Kebbi, na daga cikin murnar ranar yawon bu?e ido ta duniya, da akayi bikin murnar zagayowar ta a Birnin-Kebbi a ranar Litinin.
Dayake jawabi a lokacin taron, Sarkin yace an baiwa ministan sarautar sakamakon ?arfin gwuiwa da yake dashi wajen cigaban al’adun ?asa ya zuwa matakin duniya.
Mai martaba sarkin yace masarautar ta girmama ministan da sarautar a matsayin godiya ga ?o?arin shi, na inganta harkokin al’adu a lokacin bikin baje kolin al’adu da kama kifi na Argungu, domin ya zama dai-dai da duniya.
Kamfanin Dillancin Labaru na ?asa ya ruwaito cewar, bikin Argungu ya samu halartar ba?i daga gida da wajen ?asar.
Sarkin ya kuma yabawa Ministocin ya?a labaru da suka wuce a ?o?arin su na inganta harkokin al’adu a ?asar tun shekarar 1970.
“A madadin al’ummar masarautar ina yi maka barka da zuwa, kuma muna baka tabbacin cewa, zamu ri?a sanya ka a dukkanin abun da ya shafi masarautar,”inji shi.
Uban ?asar ya bu?aci ministan daya amshi karamcin ta hanyar cigaba da inganta harkokin al’adu a Kebbi da Masarautar Argungu gaba ?aya.
Ya bada tabbacin cewa masarautar da ?asa zasu cigaba da amfana da ?umbin ilmi da Ministan ke gareshi.
Ministan ya godema Sarkin da Al’ummar Argungu gaba ?aya da soyayyar da suka nuna mashi, musamman wajen girmama shi da suka yi ta hanyar bashi Sarautar.
