Bauchi: Ba Mu Da Amfani Sai Zabe Ya Zo – Al’ummar Birshin Fulani

Al’ummar Unguwan Birshin Fulani dake cikin karamar hukumar Bauchi sunyi Allah wadai da rashin ko in kula da zababbun shuwagabanin su masu rike da madafan iko a Jihar Bauchi suke nunawa, musamman na yankin mazabar su, kan diran mikiya, da kuma dauki daiadai da Yan’bindiga da masu garkuwa da mutane suke kai wa a wan nan Unguwar lokaci zuwa lokaci.

Rahotanni sunyi nuni da cewa harin da masu garkuwa da mutane suka kai a yankin shine karo na biyar a cikin kankanin lokaci, Wanda hakan ya fusata matasa a yankin sukayi dirshan akan babban titin hanyan Bauchi–Dass da nuna alhininsu tare da yin korafi ga Jami’an tsaro da shuwagabannin su a matakai dabam dabam na rashin katabus a kan wan nan lamarin tsaro da yayi kamari a Unguwar birshin Fulani

Wan nan sakon yana kunshe ne a wata takardar sanarwa da matasan yankin suka fitar, tare da sa hannun Shugaban matasan yankin Abdulhamid Jibrin Birshi, bayan zanga-zangar fushi da suka yi a washegarin da aka kai harin, Kuma suka turawa manema labarai a garin Bauchi.

Suka kara da cewa tunda matsalar tsaron ya fara a yankin, dan majalisa tilo daya ne kawai ya kai masa ziyarar jaje Kan al’amarin.

Sanarwar tace, ” ranar 9 ga watan satumba me 2021 yan’harin suka bindige wani Malamin makarantar kimiya da fasaha ta gwamnatin tarayya, har lahira, suka yi gaba da makubcinsa da suke hutawa tare, Suka sake dawowa Suka kashe Limamin Masallachi a garin, Suka yi awun gaba da Dan’sa da wani mutum, Saida ga baya aka biya kudi mai yawan gaske kafin suka sako su”.

Har’ila yau bayan “kwanaki kadan suka sake dawowa suka yi harbe harben bindiga a sama don razanar da mutanen garin, kafin suka arce da mutum biyu, sai da aka biya kudin fansa mai yawa kafin suka sake su suka dawo”.

Bugu da kari, a karo na UKu 3 suka sake dauke wani mutum a yankin, na Hudun 4 kuwa shine Wanda sukayi sanda suka shiga garin suka dauki matar wani ma’aikacin gidan talabijin na AIT da cikin wata takwas 8 a ranar sha bakwai 17 ga wan nan watan na Satumba, since sai annbiya su naira miliyan Hamsin 50 kafinnsu sako matar mai cikin wata takwas.

Haka na baya-bayan nan kuma shine karo na biyar 5, “yan bindigan sunyi diran mikiya a kusa da Birshin Fulanin, wato Unguwan Kanawa, inda nan ma Yan bindigan sunje sunndaki wani magidanci inda aka yi bata Kashi da su day Yan Banga a garin inda suka sha da kyar, hakan yasa matasan suka harzika suka yi zanga zanga a kan titi” Suka ce.

Yan’bindigan Sunsha alwashi cikin Kwan daya in ba a Kai masu kudin ba zasu halaka matar mai ciki, da take hannunsu

Matasan since basubga wani Mai mukami yazo masu jaje ba diknda kasancewarau cikin garin kusa da fadar jihar I’m bandabdan majalisar jiha Kuma mataimakin kakakin majalisar Jihar Danlami Kawule shi kai’da suka gani, saboda haka Suka ce basu da amfani ga zababbun shuwagabanin su kamandaga Gwamna, Sanatan yankinsu, da Kuma dannmajalisar tarayya duk na yankinsu basu ga kowa ba ko sako,

Suka ce sai lokacin zabe kaga sun shawo manyan rigunansu suna neman kuri’arsu, acewarsu lokacin ne zasuyi masu amfani, Amma ga matsalar tsaro sunyi biris da maganan kaman basu ba

Kana Sanarwar ta kara da cewa “tuni masu hannu da shuni na yankin Birshin Fulanin suka fara tattara yana su yanas u suna barin Unguwar don kar yan bindiga suyi garkuwan dasu, su kuma talakwa ko oho”. Inji matasan yankin.

Matasan suka ce yanzu haka talakwan birshin Fulanin suma sun fara shiga cikin jeji su kwan don gudun yan’bindigan a cewarsu in Suka shigo sun san Babu wani tsaro daga hukuma a yankin, cewa zasu iya cin karen su babu babbaka.

A karshe Sanarwar tace wan nan rashin ko in kula da rashin tausayawa daga shuwagabaninsu na siyasa sike nunawa, yasa ala tilas basu da wani zabi saidai abinda hali yayi.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Related posts

Leave a Comment