Dalilin Da Ya Sa Gwamnoni Ba Su Sanya Hannu A Hukuncin Kisa – Ganduje

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnoni na matukar tsoron sa hannu kan hukuncin kisa saboda ba za su so bayan kaddamar da hukunci ba daga baya a gane cewa wanda aka kashen bai dace da hukuncin ba.

An dade ana caccakar Gwamnonin kasar nan kan jinkirin da suke yi wurin sa hannu kan aiwatar da wasu hukunce-hukuncen kotu, lamarin da ake alakanta shi da dalilin cikar gidajen gyaran hali a fadin kasar nan.

Amma a yayin amsa tambayar da Trust TV ta yi wa Gwamna Ganduje a wata tattaunawa, ya ce suna tsoron sa hannu kan hukuncin kisa saboda da yawa daga cikin tsarin shari’a “abun zargi ne.”

An ruwaito cewa, ya tuna wani lamari da ya hada da tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole, ya ce, “Akwai wani lokaci da ya saka hannu kan hukuncin kisa kuma aka kashe mutumin. Daga bisani, an gano cewa bai dace a kashe shi ba. Hukuncin ya na da matsala.”

Ya ce bayan faruwar lamarin, gwamnoni sun kara kiyayewa wurin sa hannu kan hukuncin kisa, inda ya kara da cewa: “Lokaci zuwa lokaci muna saka hannu, amma idan muka yi tunanin cewa ya dace a sake duba lamarin domin sake bincike, da yawa mu kan gano cewa bai dace a kashe su ba. Idan kuma aka kashe, ba za a iya dawo da rayuwa ba.”

Related posts

Leave a Comment