Duk Dan Majalisa Na Daukar Miliyan 100 Na Ayyukan Mazabu – Dan Majalisa

Dan Majalisa Mai wakiltar Kananan Hukumomin Numan da Demsa da Lamurde a Majalisar Dokoki ta Kasa na Jahar Adamawa, Kwamoti Laori ya dora alhakin yadda ake kin tabbatar da tsarin Kasafin Kudi ya kawo rashin bunkasar tattalin arziki a Kasar.

Acewar sa, kowane Dan Majalisar Dokoki ta Kasa na samun Naira Miliyan 100 domin gudanar da ayyuka a Mazabun su.

Ya kuma bayyana rashin jindadin sa, na yadda rashin tabbatar da bin tsarin Kasafin Kudi, da wuya Dan Majalisa ya samu sama da Naira Miliyan 80 daga cikin Miliyan 100 da aka ware mashi.

Dan Majalisar ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga Manema Labaru a Yola, biyo bayan kaddamar da wasu Famfunan samar da ruwa mai amfani da hasken rana, da cibiyan Na’ura Mai Kwakwalwa, da dakiin taro dana zana jarabawa a Lafia, da Demsa da Ndem da Imburu da kuma Bali gami da Kpasham na mazabun shi, dake Kananan Hukumomin Lamurde da Demsa da Kuma Numan.

Laori yace “idan kaje ka duba abunda yake Ayyukan mu, bai kamata mu Shiga cikin harkar kawo gine-gine da kayan bukatun rayuwa a Mazabun mu. Amma sabudda rashin tabbatar da tsarin Kasafin Kudi, Wanda ya kamata ya kawo wannan ababen, ta sanya dole mun shiga cikin bayar da wadannan abubuwa domin cike guraben da aka rasa.

“Ta bangaren kudi, kowane Dan Majalisa ana bashi Naira Miliyan 100. Wadannan kudade ana amfani dasu domin gudanar da ayyukan cigaba a Mazabu.

Related posts

Leave a Comment