Da Dumi-Dumi: An Tsige Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi


Rahotanni daga Birnin Kebbi babban birnin Jihar Kebbi na bayyana cewar an tumbuke Shugaban Majalissar dokokin jihar Kebbi Isma’il Abdulmiminu Kamba, daga mukamin shi.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalissar jihar Mohammed Tukur Shanga ne, ya bayyana tumbuke Kamba daga Mukaminsa, ya yin da yake zanta wa da manema labarai yau Talata, a zauren majalissar.

Ya ce, ya zama wajibi a cire kakakin majalissar Dokokin jihar Kebbi, saboda kin bin ka’idojin doka, da kuma saba wa wasu tsare-tsare.

Shanga ya bayyana cewa, 21 daga cikin mambobin majalissar 24 ,sun sanya hannu kan takaddar cire kakakin majalissar, ya yin da sauran ukun suka ki amince wa.

Kazalika ya ce tuni majalissar ta rantsar da sabon Shugaban majalissar, wanda kuma ya yi alkawarin jagorantar majalissar kamar yadda ya dace.

“Sabon kakakin majalissar mu shi ne Mohammad Abubakar Lolo daga mazabar Bagudo, Kuma mun amince da shi, kana a shirye muke mu tallafami shi wurin gudanar da aiyukan shi” inji shi.

Related posts

Leave a Comment