Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya a ranar Litinin 23 ga watan Agustan 2021 ta fara kaddamar da shirin N-Power rukunin C shashi na farko.
Ma’aikatar agaji da ayyukan jin kai ta kasa ta fara aikin yin rajista na rukuni na uku na masu cin gajiyar shirin a ranar 26 ga Yuni, 2020.
Ministar agaji da ayyukan jin kai, Sadiya Farouq ta ce sama da mutum miliyan shida suka nuna sha’awarsu ga cin gajiyar shirin.
Ta ce rukunin C zai dauki mutane 510,000 don cin gajiyar shirin sashi na farko da kuma mutane 490,000 a sashi na biyu.
Ta ci gaba da bayanin cewa a karkashin Batch C1, an zabi 450,000 don amfana a karkashin bangaren masu digiri yayin da masu cin gajiyar 60,000 za su zama wadanda ba su kammala karatun ba.
A cewar Ministar, a karkashin bangarorin da suka kammala karatun digiri, masu cin gajiyar shirin za su rika samun alawus na wata-wata na N30,000 yayin da sabanin su za a rika biyan su N10,000 a kowane wata.
An kirkiro shirin ne don taimakawa matasa ‘yan Najeriya su samu da kuma habaka kwarewarsu a rayuwa don zama kwararru a kasuwannin cikin gida da na duniya. Ana sa ran wadanda za su ci gajiyar shirin za su dukufa a fannonin ilimi, noma, kiwon lafiya, gini, ICT da fannonin masana’antu.
Da take magana game da shirin, Sadiya ta ce: “Duk masu cin gajiyar shirin ana ba su jari don ba su damar fara kasuwancin a cikin sana’o’in da suka zaba.” Don tabbatar da biyan kudi ta tsarin bayanai ba tare da bata lokaci ba, ministar ya kuma ce an kaddamar da wasu tsare-tsare ta kafar NASIMS) tare da hadin gwiwar manyan MDAs ciki har da NYSC, UBEC, NPHCDA, NOA don aiwatar da ayyukan yadda ya kamata.
An sanar da mataki na gaba a shirin N-Power na gwamnatin Buhari Ma’aikatar Aikin Jin Kai da Ci Gaban Jama’a ta sanar da mataki na gaba ga masu neman shiga shirin N-Power karkashin rukunin C sashi na farko. Babban Sakatare, Bashir Alkali, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi ya ce ma’aikatar ta fara mataki na gaba na yin rajista tare da tabbatar da adiresoshin imel ta masu neman shiga shirin.
