Rikicin babbar jam’iyyar hamayya PDP ya sake ?aukar wani sabon salo ranar Litinin yayin da wata babbar kotu a jihar Ribas ta dakatar da Uche Secondus daga bayyana kansa a matsayin shugaban PDP na kasa.
Secondus, wanda yake ta fa?i tashin rike mukaminsa, an ba shi damar ya shirya gangamin taron jam’iyyar a watan Oktoba.
Rahotanni sun bayyana cewa Secondus ya matsa cewa dole a barshi ya karasa wa’adin mulkinsa kamar yadda doka ta tanada.
Mai shari’a O. Gbasam, ya tum?uke Uche Secondus daga matsayin shugaban PDP yayin da yake yanke hukunci kan karar da jiga-jigan PDP suka shigar akansa.
Wa?anda suka shigar da karar sun ha?a da, Ibeawuchi Ernest Alex, Dennis Nna Amadi, Emmanuel Stephen da kuma Umezirike Onucha.
Alkalin kotun ya kuma hana Secondus jagorantar shirya gangamin taron PDP na gundumomi da na kananan hukumomi, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
Wani sashin jawabin Alkalin yace: “Kotu ta bada umarnin hana wanda ake kara daga bayyana kanshi a matsayin shugaba ko kuma gudanar da ayyukan shugaba.” “Hakanan kotu ta umarci hana wanda ake kara kira, halarta ko jagorantar wani taro ko shiga wani kwamiti a matakin gunduma, karamar hukuma ko jiha.
“Kuma an hana wanda ake kara daga shirya gangamin taron gundumomi, kananan hukumomi ko jiha yayin da aka dakatar da shi daga kasancewa ?an jam’iyya.”
