Yada Hotunan Batsa: Kotu Ta Yankewa Jarumar Hausa Fim Hukunci

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta garkame wata ?ar wasan Kannywood da kuma ta yi fice a kafar sada zumunta, Sadiya Haruna kan ya?a hotunan batsa a shafukanta na sada zumunta.

Tun a ranar Juma’a aka kama Sadiya Haruna mazauniyar Kabuga da ke Kano.

Aka kuma ci gaba da rike ta har zuwa wannan Litinin ?in tare da gabatar da ita a kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Sharada.

Sadiya ta amsa laifi guda cikin tuhume-tuhumen da aka gabatar a kanta, wanda ya ci karo da sashi na 355 na kudin panal code na 2000.

Mai shari’a Ali Jibril Danzaki ya yanke mata hukunci tare da umartar ta koma Islamiyya tayi karatu na tsawon wata shida.

Sannan ya ce a kullum za ta rin?a zuwa Islamiyyar da rakiyar jami’in Hisbah da kuma sa idon shugaban makarantar.

Related posts

Leave a Comment