Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, a ranar Lahadi, yace shugabannin arewa ke da alhakin matsalar tsaron da ya mamaye yankin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Matawalle ya yi wannan hangen ne yayin da yake gabatar da wata takarda mai taken “Yaki da yan bindiga a yankin arewa maso yamma: ?alubale da hanyar warware su” a wurin taron ?addamar da sabbin shugabannin ?ungiyar marubutan Arewa “Arewa Media Writers” a jihar Kaduna.
Yace shugabannin Arewa suke da alhakin yanayin da yankin ke ciki, wanda ya ha?a da aikata manyan laifuka kamar fya?e, kisan mata da ?ananan yara, sace mutane, fashi da makami da sauran manyan laifukan da suka mamaye yankin.
A cewar gwamnan, arewa ta rasa kyakkyawan shugabancin da zai jagoranci gina yankin da magance matsalolinsa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Ya kuma ?ara da cewa manyan masu fa?a a ji na yankin arewa ba su da wani kudiri face su samu damar ?arewa kan mulkin siyasa.
Matsalar Da Zamfara Ke Ciki
Matawalle yace lokacin da ya amshi mulki a 29 ga watan Mayu 2019, Zamfara ta riga ta shiga halin ?a?anikayi na rashin tsaro da ya shafe lokaci mai tsawo.
Gwamnan yace jihar bata da wani labari a kullum kwana sai na zubar da jini, wuta, sace-sace da kuma korar mutane daga mahallinsu musamman wa?anda ke rayuwa a yankunan karkara.
Gwamna Matawalle, wanda kwamishinan ya?a labarai na jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Magaji, ya wakilta, yace: “Rikicin ya kawo karuwar talakawa da kuma rashin abinci, Zamfara ta kama hanyar rugujewa ta kowane ?angare saboda tada zaune tsaye a yankunan karkarar mu da ma Arewa baki ?aya.”
“?ananan hukumomin Shinkafi da Zurmi sun zama gidan aikata ta’addancin yan bindiga duka da cewa an daina ha?ar ma’adanai a yankunan.”
Arewa Ta Rasa Masu Tallafawa
Gwamnan ya koka kan rashin masu taimakawa daga ?angarorin yan siyasa, wa?anda ke amfani da wannan damar wajen cimma wani kudirinsu na siyasa.
Yace: “Dukkan mu munga yanda manyan kudu-gabas da kudu-yamma suka ?auki mataki cikin ha?in kai a kan duk abinda ya taso a yankinsu.”
“Munga yadda suke da manufa ?aya kuma basu gajiyawa wajen kokarin kawo cigaba a yankinsu.
Matawalle ya yi kira ga manyan shugabannin yankin arewa da su farka daga baccin da suke, su ha?a kansu domin fuskantar duk wani ?alubale.
