Tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari, ya bayyana cewa, ‘yan siyasa na yin lissafi da gwagwarmaya ne amma dukkan karfi da mulki na Allah Ma?aukaki ne.
A cewar Yari, wanda ya kasance tsohon Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ne, da zarar Mai Iko Dukka ya amince da burinsa na Shugabantar APC, babu wani ?an siyasar da zai iya dakatar da hakan.
“Ina da cikakken imani ga Allah Ma?aukaki, kuma na aminta da adadi mai yawa na mutane, gami da duk wa?anda suka nuna amincewa da ni a baya, idan Allah ya ce zan zama Shugaban APC, babu wanda zai iya dakatar da ni, kuma duk na shirya cin nasara,”
Yari ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.
Da yake ci gaba da magana, ya ce, akwai wasu rikice-rikice a yakin neman shugabancin jam’iyyar APC mai mulki amma sai dai ?an gwagwarmaya da ke jin tasirin jama’a kuma yana da gogewar da ta gabata a yakin siyasa ne zai iya kai jam’iyyar ga nasara a 2023.
Alhaji Yari ya kuma jaddada cewa, bai damu da jita-jitar da ake ya?awa ba na cewa wasu masu rike da mukamai ko tsoffin gwamnoni a yankin Arewa maso Yamma na iya tsunduma cikin wani shiri na yin ?afar ungulu ga burin shugabancinsa don tabbatar da cewa daya daga cikinsu ya zama Shugaban qasa ko Mataimakin Shugaban ?asa a 2023.
“Wani ya fa?a min cewa wasu abokan aikina da tsoffin abokan aiki na suna da ra’ayi na daya da na biyu, saboda haka, idan kujerar Shugabancin ?asa ta koma yankin Arewa maso Yamma, babu abin da zai same su, don haka suka ha?a kai don kashe Yari.” “Idan Allah ya ?addara hakan ta kasance, abin zai kasance.
Mutane na iya ?ir?ira su yi kowane irin lissafi amma ba za su yi nasara ba. Abin da na sani kawai shi ne, ina da ?arfin da zan jagoranci wannan jam’iyyar kuma sun san abin da zan iya yi,” in ji shi.
A cewar Alhaji Yari, duk da rashin iya aiwatar da duk wasu manufofin da ta sanya a gaba a manufofinta na ci gaba, APC na da dimbin damar cin za?en 2023 ta hanyar da ke da matu?ar birgewa, idan aka yi abin da ya dace daga yanzu zuwa na gaba.
Ya nanata cewa, ?aya daga cikin abubuwan da ya kamata APC ta yi shi ne baiwa jam’iyya mai ?arfin hankali da kwatankwacin mutane irinsa damar maimaita nasarorin za?en da ya gabata wanda ya cimma tun kafin fara mulkin dimokura?iyya a yanzu.
Idan ya koma baya, sai ya tuno da matsayinsa na matashin dan siyasa a lokacin shekarun mulkin Abacha da kuma ?ir?irar rusasshiyar jam’iyyar APP wanda ya sanya shi Sakataren ta na Jiha da kuma Darakta Janar na gwamnoni da ya?in neman za?en shugaban ?asa a zahiri, wanda ya kasance gagarumar nasarar zabe ne a jihar Zamfara.
Yari ya kuma yi watsi da zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi masa a matsayin ?azantar siyasa daga mutane marasa fuska, ya ?ara da cewa, kasancewar ya yi iya bakin ?o?arinsa a matsayinsa na ?an majalisar wakilai, gwamnan jihar kuma shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya, ba shi da bukatar damuwa, da kuma binciken da hukumar EFCC ke gudanarwa kan gwamnatinsa.
“Wasu mutane na iya ?ir?irar ?arya amma a ?arshen rana, gaskiya za ta yi halinta. Akwai sauran abubuwa da yawa da suka fada wadanda kawai wasu maganganun karya ne da ake son a kawo mutumin kirki baya, amma ba za su ta?a yin nasara ba,” in ji yari.
