Rahotanni daga Jihar Legas na bayyana cewar Chief Ayo Adebanjo, shugaban kungiyar Afenifere, kungiyar Yarbawa zalla kan zamantakewa da siyasa, ya ce gwamnatin tarayya ba ta da hurumin neman a dawo da Sunday Igboho daga Jamhuriyar Benin, kuma kama shi da aka yi abin Allah wadai ne.
Bayan ‘yan makwanni da jami’an tsaro na farin kaya (DSS) suka bayyana neman Ighoho “ruwa a Jalo”, jami’an tsaron Jamhuriyar Benin sun kame shi a birnin Cotonou yayin da yake kokarin tserewa zuwa kasar Jamus.
Mahukuntan Najeriya na ci gaba da matsa kaimi wajen ganin an dawo da dan rajin neman kafa kasar Yarbawa daga kasar ta Benin mai makwabtaka da Najeriya domin fuskantar hukunci.
Kamun na Igboho ya haifar da martani daga fitattun mutane a Najeriya, musamman daga yankin Kudu maso Yammacin kasar wato Jihohin Yarbawa zalla.
A ranar Alhamis, a cikin hira da tashar Arise TV, Adebanjo ya daga muryarsa ga masu yin martani kan kamen Igbohon. Ya bayyana Igboho a matsayin “fursunan siyasa”, kuma ya ce gwamnatin tarayya ba ta da ”izinin neman tasa keyarsa zuwa Najeriya.’
Shugaban na Afenifere mai shekara 93 ya ce hukumomin Najeriya kawai suna tsoro da fargabar shaharar Igboho ne kawai, yana mai cewa “mahukunta na son kashe shi saboda yana jagorantar tawayen jama’a”.
Ya ce, “Buhari na iya dogaro da ‘yan kanzaginsa, amma mu muna da Allah. Kuma muna kira ga Allahnmu da Ya yi mana maganin Buhari ”. “Shi [Igboho] dan gudun hijirar siyasa ne. Bai aikata wani laifi a nan ba.
Bai jagoranci kashe kowa ba. Bai tserewa kowa ba baya aikata laifi. Ya gudu domin ransa saboda masu iko na son kashe shi saboda fafutikar da yake yi. Yana kuma jagorantar wani tawayen da al’umma ke yi, ”in ji Adebanjo.
