Bauchi: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Matashin Dan Siyasa

Matashin dan Siyasa mai suna Uba Boris a garin Bauchi Yan’bindiga sunkai mashi hari wadan da ba asan ko suwanene ba sunyi awon gaba dashi jiya bayan Sallar magariba a daidai gidan mai na A A Rano daura da shatale talen babban bankin Najeriya (CBN)

Wan nan dansiyasa ya rike mukamin maitallafa ma tsohon gwamnan Jihar Malam Isah Yuguda ta fanin matasa sun mashi kawanya tare da harba bindiga sama domin tarwatsa jama’a a lokacin misalin karfe takwas 8:00 na daren jiya

A ta bakin wadanda suka gane ma idansu abin da ya faru, sunce maharan suna kan mashinan guda biyu ne suna biye dashi a kanntitin Nasarawa sukasha gabansa tare da harbe harben bindiga don tarwatsa jama’a

Mutanen da suka ga abin, sun kara da cewa a daidai lokacin da suka dauke shi sun jefa shi cikin wata mota ta daban a bakin hanya Kuma sunci gabanda harba bindiga sama har suka bache ba aganinsu

Mutane a bakin titin sun ce da maharan sun nufi hanyar titin Nasarawa sai suka ga motar patrol ta Yan’sanda a tsaye sai suka juya da gudun tsiya kafin yan’sandan su ankara har sunyi layar zana ta hanyar Federal Low-cost

Bugu da kari wani shima Wanda yaga yan’bindigan yace yana tsaye a wajen sayar da motoci tukunbu zasunyi Sallar Isha’i kawai suka ji harbi ta koa ina ana harbawa sama har suka wuce dashi, suka bache bat tare a cikin motarsu

Shidai Uba Boris ya sanu ne a fageYa rike mukamin Shugaban tsare tsare na makarantar (Yuguda Vocational Center) a turance, inda ake koyar ma da matasa sana’oi dabam-dabam duk dai a siyasan ce.

Kuma har ila yau, a yanzu haka shi mairuwa da tsaki ne a babbar jamiyyar adawa a Jihar ta APC a bangaren matasa a siyasar Jihar

Muryar Yanci’ tayi kokarin jin ta bakin yan’uwanshi ko abokan siyasar shi don jin ko sun sami labarin sa zuwa yau ranar Alhamis, sunce har yanzu babu labarinsa daga wajen Yan’bindigan amma suna nan suna sa Ido

Hakanan munyi kokarin jin ta bakin Yan’sandan jihar ko akwai wani karin bayani shiru kake ji, inda kakkin Yan’sanda Ahmed Wakil bai amsa kirar waya da Yan’jarida suka yi ba, tare da aika sakon kar ta kwana, amma shiru babu amsa.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Related posts

Leave a Comment