Naji Dadin Cafke Nnamdi Kanu Da Aka Yi – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana farin cikinsa game da kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar Tsagerun Inyamurai masu han?oron kafa kasar Biyafira (IPOB).

Da ya ke tsokaci a kan kamen lokacin da aka yi hira da shi a BBC Pidgin a ranar Juma’a, El-Rufai ya ce ya yi murna da kama Kanu saboda ya tsere bayan bashi beli sannan yana kiran Nigeria ‘Zoo’ wato gidan namun daji.

“Na yi farin ciki sosai (lokacin da aka kama Nnamdi Kanu) saboda, da farko ya tsere bayan bashi beli, ya saka wadanda suka tsaya masa cikin matsala. “Na biyu, yana kallubalantar iko da hukumomin kasa mai zaman kanta kuma yana tada rikici; yana kiran kasarsa a matsayin Zoo.

“Ya kamata wannan ya zama darasi ga dukkan wadanda ke ?alubalantar ikon da kasar Nigeria ke da shi, su yi takatsantsan.”

Related posts

Leave a Comment