Gwamnatin Jihar Katsina ta cire kashi 3% daga cikin albashin ma’aikatan jihar na watan Yuni, a matsayin gudummawa ga wa?anda lamarin iftila’i ya rutsa da su a kasuwar ta Katsina.
Katsina Post ta samu labarin cewa ma’aikatan jihar da suka amshi albashin watan Yuni, tuni suka lura da ragin ku?in a asusunsu,
Ku tuna cewa gwamnatin jihar Katsina ta sanar da cewa dukkan ?angarorin ma’aikatan gwamnati da masu ri?e da mu?aman siyasa, za su bayar da gudummawar wani ?angare na albashinsu, don tallafawa wa?anda iftila’in gobara ya shafa a babbar kasuwar Katsina.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa “za a cire kaso uku daga albashin dukkan Ma’aikatan Gwamnati daga matakan 01 zuwa 14 yayin da za a cire kashi 20 cikin 100 daga albashin Gwamna da na mambobin majalisar zartarwa. Amma ragowar zai kasance na wata ?aya ne ka?ai”.
