Tsadar Abinci: Babban Bankin Najeriya Zai Karya Farashin Shinkafa

A kokarinsu na samar da wadataccen abinci ga ‘yan Nijeriya tare da karya farashin shinkafa, Babban Bankin Nijeriya (CBN) da Kungiyar Manoman Shinkafa ta Nijeriya, sun fara batun kaddamar da sayar da tan miliyan tara na tallafin shinkafa ga masu sarrafata.

Gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele yayin da yake kaddamar da shirin sayarwar da kuma fara noman rani a Kaduna ya ce, bankin a shirye yake ko yaushe don tallafawa harkar noma.

Ahmed Mohammed na CBN reshen jihar wanda ya wakilci gwamnan, ya ce shirin an shirya shi ne don sayar da shinkafar a kan farashi mai rahusa da nufin karya farashin don amfanin kowa a Nijeriya da ma wasu kasashen.

Gwamnan Babban Bankin ya ce, bankin a shirye yake domin tabbatar da wadatar abinci da inganta noman shinkafa a kasar.

Related posts

Leave a Comment