Gwamna Matawalle Shine Jagoran APC Yanzu A Zamfara – Mai Mala Buni

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Shugaban ri?o na jam’iyyar APC ta ?asa kuma gwamnan jihar Yobe Maimala Buni ya ce daga yau Gwamna Bello Matawalle ne jagoran jam’iyyar a jihar Zamfara.

Hakan na ?unshe ne a wata sanarwa da gwamnatin jihar Zamfara ta fitar jim ka?an bayan komawar Matawalle APC a yau Talata.

Sanarwar mai ?auke da sa hannun mai taimaka wa gwamnan na musamman kan harkokin watsa labarai Zailani Baffa, ta ambato Mai Mala na cewa: “Daga yanzu Matawalle ne jagoran jam’iyyarmu mai girma a jihar Zamfara.”

“Za ku saurari sauran shirye-shirye na samar da sabuwar jam’iyya daga wajensa nan gaba ka?an,” in ji Buni.

A lokacin da yake kar?ar tutar jam’iyyar, Gwamna Matawalle ya kar?i jagorancinta a yayin da ya ayyana kansa a matsayin mamba a cikinta.

Kazalika Gwamna Matawalle ya shiga jam’iyyar ne tare da dukkan sanatocin jihar da ke kan mulki a yanzu, da ?an majalisar wakilan tarayya shida daga cikin bakwai da kuma dukkan ?an majalisar dokokin jihar.

Da yake magana a wajen taron sauya she?ar, tsohon gwaman Zamfara Abdulazeez Yari, ya ayyana goyon bayansa da kuma jajircewa don samun nasarar jam’iyyar, tare da addu’ar neman tsarin Allah daga duk wata masifa da za ta sake samun jam’iyyar.

Daga cikin wa?anda suka halarci bikin sauya sheka?ar har da gwamnonin Kano da Kaduna da Kebbi da Borno da Kogi da Neja da Yobe da Ogun da Katsina da Jigawa da kuma Filato.

Sannan tsohon gwamnan jihar Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ma ya halarta.

Related posts

Leave a Comment