2023: Zabena Shi Ne Mafita A Najeriya – Tinubu

Labarin dake shigo mana daga Jihar Legas na bayyana cewar Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce Najeriya na bukatar shugaba mai jajircewa wajen aiwatar da sauye-sauyen da za su kawo kudaden shiga da gina kasa kamarsa.

Ya bayyana kansa a matsayin mutumin da Najeriya ke bukata a tafiyar ta zuwa garin harkokin ci gaba. Tinubu yayi magana ne a wajen taron kwana daya tsakanin shugabannin majalisar wakilai da mataimakansu na Jihohin da APC ke jagoranta.

Kakakin majalisar dokokin Legas Mudashiru Obasa ne ya karbi bakuncin taron wanda ya gudana a birnin Ikko babban birnin jihar ta Legas.

“Najeriya na bukata ta kamar yadda nake bukatar Najeriya. Najeriya na bukatar tsattsauran sauye-sauye masu kyau da za su kawo kudaden shiga kuma ni ne mai jajircewar da take bukata.”

Hakazalika, Tinubu ya siffanta kansa a matsayin mutumin da ya gina rayuwarsa akan jajircewa, don haka Najeriya ke bukatar mutum irinsa. Ya kara da cewa: “Hanzarta ciyar da al’ummarmu gaba batu ne na tunani da aiki, kuma a shirye nake in sake yin hakan saboda ni mai tunani ne kuma mai aikatawa.”

Ya kuma roki ‘yan majalisar da suka ziyarce shi da kada su tsaya su kadai, su tsaya tsayin daka, su hada kai, su zama daya, domin aikin mayar da Najeriya wacce ta ke kasa daya.

Shugaban taron, kuma kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, ya bayyana cewa ‘yan majalisar dokokin jihar na da matukar muhimmanci a harkokin dimokuradiyya a matsayin wadanda suka fi kowa kusanci da jama’a.

Suleiman ya bayyana Tinubu a matsayin babban jigo mai hali da sadaukarwa, wanda ke ba da fifiko ga jin dadin ‘yan jam’iyyarsa.

Related posts

Leave a Comment