Gwamnatin jihar Kaduna ta nuna damuwan ta kan karuwar kwalejojin kiwon lafiya masu zaman kansu da asibitoci marasa lasisi, tana mai cewa nan ba da jimawa ba, za ta fara rufe irin wadannan cibiyoyi a jihar.
Kwamishinar lafiya, Dakta Amina Baloni, ce ta bayyana hakan, yayin da take amsa tambayoyi daga manema labarai a Taron manemai labarai na kwana daya da ya gudana a jihar mai taken, Inganta Fannin Lafiya ta hanyar aiwatar da Asusun Bayar tallafi ga Asibitocin Kula da Lafiya, wanda Gidauniyar Save the Children ke ta dauki nauyi a jihar.
Ta ce tuni jihar ta fara bincike don sanin ainihin adadin makarantun Horas da Fannin kiwon lafiya marasa lasisi a jihar.
Wadanda ba su yi rijista ba za a nemi su zo su yi, don kada lokacin da za mu fita, kada wani ya zo ya sa baki. Sharu??an bu?e makaranta ba ?aya suke da bu?e asibiti ba inji ta.
Kazalika Kwamishiniyar ta ce, Don kawai ina da lasisi a matsayin likitan, ba yana nufin zan iya zuwa in bu?e makarantar likitanci, ko kuma cewa ke maaikaciyar jinya ce, za ki iya bu?e makarantar jinya ba,

