Site icon Muryar 'Yanci

Za A Kashe Naira Biliyan 25 Wajen Inganta Lafiya A Najeriya

images 2024 03 12T063814.559

Ministan lafiya da Walwalar Jama’a, Ali Pate, ne ya bayyana hakan sa’ilin da yake jaddada aniyar gwamnatin Shugaba Tinubu ta yiwa harkar kiwon lafiyar ‘yan Najeriya garanbawul ta yadda zai dace dana sauran duniya.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin ma’aikatar, Deworitshe Patricia, ta fitar a jiya Lahadi a Abuja, Ministan yace, ba za’a iya samun nasarar yiwa harkar kiwon lafiya garanbawul da sabunta shi harma da samar da karin damammaki ba har sai an samu amincewar tsarin nan na hannu da yawa a bangaren lafiya (SWAP) da kuma tsarin sabunta zuba jari a bangaren lafiya (NHSRIP).

A cewar Ministan game da cigaban da aka samu a fannin kiwon lafiya a matakin farko a Najeriya a bisa tsarin swap, na hannu da yawa, nazarin da aka gudanar ya bayyana bukatar yin kwaskwarima ga tsarin gudanar da asusun kula da kiwon lafiya a matakin farko (BHCPF) da tsare-tsare da ayyukansa da tsarin bin diddigin yadda ake kashe kudade da kimarsa a idanun jama’a, inda yace dukkanin jihohin Najeriya da Abuja sun dukufa wajen kawo gyara, tare da shan alwashin inganta kiwon lafiyar ‘yan Najeriya.

Exit mobile version