Kwamitin da ke yakar annobar korona a Najeriya ya haramtawa mutum dubu biyu shige da fice a kasar na tsawon shekara guda, saboda kaucewa gwajin annobar korona a tashoshin jiragen saman kasar.
Shugaban kwamitin, Mukhtar Muhammad ne ya shaida hakan a Abuja lokacin ganawa da manema labarai.
Muhammad ya ce sun wallafa sunayen wadanan mutanen bayan samun bayanansu daga jami’an da ya kamata suke bincike da gwaji kan ‘yan Najeriya da baki da ke shigowa kasar, sakamakon sake barkewar anobar korona karo na uku.
Ya ce gwamnati ta dage akan cewa duk wani fasinja da ya shiga kasar, musamman daga kasashen da ke cikin barazana, dole su killace kansu a wuraren da gwamnati ta tanada, kuma an kwace fasfon mutanen da suka ki mutunta wannan doka na tsawon shekara guda.

