Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ?an ta’adda masu fashin daji sun yi garkuwa da ?an kasuwa sama da guda 70 a kan hanyar su ta zuwa Kano a titin Birnin-Gwari zuwa Kaduna a ranar Laraba.
Jaridar Vanguard ta rawiato cewa an shaidawa manema labarai a Kaduna cewa ?an ta’addan sun tare jerin-gwanon motocin ?an kasuwan ne in da daga bisani su ka yi awon-gaba da su cikin jeji.
Jaridar ta ce Rundunar ?an Sanda ta jihar ba ta ce komai a kan harin a daidai lokacin da ta wallafa labarin.
?arin bayani na nan tafe

