Rahotanni daga Jihar Bauchi na bayyana cewar a kalla mutane 20 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon kamuwa ta annobar cutar Kwalara (amai da gudawa) da ta barke a jihar ta Bauchi.
Mutane 322 ne aka ruwaito sun kamu da cutar da ta yadu a kananan hukumomi tara a jihar ta Bauchi inda ta jefa jama’a cikin mawuyacin hali na tsaka mai wuya.
Kwamishinan lafiya na jihar Bauchi, Dr Aliyu Mohammed Maigoro, shine ya bada wannan karin bayanin yayin taron manema labarai a ranar Talata.
Maigoro ya yi bayanin cewa mara lafiya na farko da aka gano tana dauke da cutar, wata ce mai shekaru 37 kuma an kwantar da ita a babban asibiti Burra a ranar 24 ga watan Afrilun 2021 a karamar hukumar Ningi.
Bayan kwantar da ita ne sai aka gano akwai bullar cutar ta amai da gudawa a wasu garuruwa da ke makwabtaka da su kamar Sumaila da wasu kananan hukumomi a Kano da akwai yiwuwar daga Bauchi abin ya yadu zuwa can.

