Site icon Muryar 'Yanci

CORONA Ta Kama Ministar Harkokin Mata

Ministar Harkokin Mata ta Najeriya Dame Pauline Tallen ta kamu da cutar nan mai sar?e numfashi ta Covid 19 wadda aka fi sani da suna CORONA.

Cikin wani sa?on Twitter da ta wallafa a ranar Lahadi, Madam Pauline ta ce gwajin da ta yi ne ya tabbatar ta kamu da cutar bayan ta yi mu’amala da wasu da suka kamu da ita.

Sai dai ba ta bayyana lokacin da ta yi gwajin ba, amma ta ce ta killace kantsa.

Kazalika ta ce iyalanta ba su kamu da cutar ba, kamar yadda nasu gwajin ya nuna.

“Ya zuwa yanzu, alamun cutar ba su bayyana a jikina ba amma na killace kaina na tsawon lokacin jinya. Ina ro?on addu’o’inku,” in ji ta.

Cutar CORONA na cigaba da mamayar mutane a Najeriya, inda a baya bayan nan cutar ta afka gidan Sakataren Gwamnatin tarayya Boss Mustapha ta kwashi hu?u daga cikin ‘ya’yan shi, sannan ta tsallaka Jihar Legas ta harbi Gwamnan Jihar, bayan ta kama manyan Janarori a rundunar sojin kasar.

Tuni dai gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta na shigo da allurar rigakafin cutar Najeriya tare da tabbatar da cewar an yi wa kowane ?an Najeriya allurar.

Exit mobile version