Site icon Muryar 'Yanci

CORONA Ta Hallaka ?anin Mataimakin Gwamnan Legas

Cutar Korona ta kashe kanin mataimakin Gwamnan jihar Lagos, Dr. Obafemi Hamzat mai suna Haroun.

Haroun Hamzat kwararren matashin likita ne dake aiki a daya daga cikin asibitocin kiwon lafiya na Gwamnati dake Orile Agege LCDA.

Margayin ya rasu ne a jiya Talata yana da shekara 37 a duniya.

Hukumar dakile yaduwar cutar korona, NCDC ta ce a jiya Talata kadai mutum 1,354 suka kamu da cutar ta Korona a Nigeria.

Ga dai jadawalin wanda suka kamu a jiya kamar haka:-
Lagos-712,
Abuja FCT-145
Plateau-117
Kwara-81
Kaduna-54
Sokoto-39
Oyo-38
Rivers-37
Gombe-21
Enugu-20
Akwa Ibom-16
Bauchi-14
Delta-14
Ebonyi-13
Anambra-9
Taraba-8
Edo-8
Kano-3
Osun-2
Ekiti-2
Ogun-1

Jummilar masu korona a Nigeria a ranar Talata
Adadin masu Korona a jiya Talata ya kai 92,705

An sallami mutum 76,396
Sannan ciwon ya kashe mutum 1,319

Exit mobile version