Site icon Muryar 'Yanci

CORONA: An Garga?i Jama’a Da Shiga Jihar Kogi

Kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar COVID-19 a ranar Litinin ya ayyana jihar Kogi a matsayin jiha mafi hadari saboda kin amincewarta na wanzuwar kwayar cutar Coronavirus, da ma yadda jihar ke kin bada rahoto na yau da kullum kan cutar, sannan ta kuma ki samar da cibiyoyin kebe masu dauke da cutar.

Manajan da ke kula da abubuwan da ke faruwa a kasa (NIM) na kwamitin PTF Dakta Mukhtar Muhammad, ne ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa a Abuja.

Mukhtar ya kuma gargadi ‘yan Nijeriya da su kauracewa ziyartar jihar don kada su fada cikin hadari.

In dai jama’a ba su mance ba Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya fito ?arara a kwanakin baya ya soki lamirin Gwamnatin Tarayya akan batun cutar ta CORONA, inda ya tabbatar da cewar CORONA ba komai ba ce face wata hanya ce ta kasuwanci.

Tun da a farkon lokacin bayyanar CORONA Gwamna Yahaya Bello ya nuna shakkun sa akai, inda ya ce babu ita a Jihar Kogi kuma babu wanda ya isa ya tursasata cikin jihar.

Exit mobile version